Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin saman Dubai ya yi hatsari a kasar Rasha


Wani Hatsarin Jirgin Sama
Wani Hatsarin Jirgin Sama

Wani jirgin saman da ya taso daga kasar Dubai ya fadi a lokacin da yake kokarin sauka birnin Rostov-Na-Danu da ke kudancin Rasha.

Jirgin kirar Boeing 738 yana dauke da kusan mutane 60 fasinsoji da ma’aikatansa.

Har yanzu ba wani bayanin wadanda hatsarin ya ritsa da su a cikinsa bisa bayanin da gwamantin kasar ta bayar. Jirgin dai na kamfanin FlyDubai ne, sannan ya bayyana a shafinsa na sada zumunci cewa sun sami labarin aukuwar hatsarin.

Jami’ai a Rostov-on-Don sun ce jirgin ya kama da wuta bayan faduwarsa, sannan ba wani jawabin musabbabin faduwar jirgin.

Amma an fadi cewa abin ya auku a lokacin da ake cikin yanayin ruwan sama da iska mai karfin gaske.

XS
SM
MD
LG