Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jirgin Saman Ethiopia Da Yayi Hatsari Yabi Duk Ka'idojin Da Ya Kamata Ya Bi


Akwai alamun cewa ma’aikatan jirgin saman Ethiopia da suka yi hatsari jim kadan bayan tashin jirigin a watan jiya, sun bi duk ka’idojin da suka dace wajen tuka jirgin kamar yadda aka umurce su da aikatawa, a cewar wani rahoto da aka fitar a yau Alhamis.

Rahoton farko da Gwamnatin kasar Habasha ta fitar, ya tabbatar da cewa ma'aikatan sun kasa sarrafa jirgin kirar Boeing 737 Max 8, bayan da ya soma tangal-tangal a sararin sama, duk da cewa sun bi duk hanyoyin da suka dace wajen tuka shi.

Duk wannan bayanin dai an same shi ne daga cikin akwatunan daukar sauti na jirgin. Kuma bayanin na karfafa tunanin rashin tabbas da masana da dama suka jima suna yi game da amincin na’urorin da ke sarrafa jirgin saman na Boeing, abinda ya janyo har kasashe da dama yanzu suka dakatar da amfani da irin wadannan jiragen tun kusan wata guda da ya gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG