Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya a Abuja wasu suka yi zanga zanga akan cin hanci da rashawa a Najeriya, matan shiya ma sun yi akan a sako shugabansu

Jiya a Abuja wasu 'yan Najeriya suka fantsama kan titunan Abuja suna nuna rashin jin dadinsu da abu da suka kira cin hanci na kin kari da ya zama ruwan dare gama gari. Haka ma matan shiya suka fita suna zanga zangar neman a sako masu shugabansu Shaikh Ibrahim El-zakzaky

Dubban mutane dauke da kwalaye da naurar kara murya suka fantsama kan titunan Abuja suna zanga zanga akan yadda cin hanci da rashawa suke kara yaduwa duk da yakin da gwamnati tayi ikirarin tana yi da wadandannan muggayen dabi'u.

Su ma matan kungiyar Shiya ba'a barsu a baya ba domin sun fito suna zanga zangar neman gwamnati ta gaggauta sako masu da shugabansu, Shaikh Ibrahim El-zakzaky, wanda take tsare dashi tun shekarar 2015

Domin Kari

XS
SM
MD
LG