Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Ba Sojin Najeriya Umurnin Koyon Harsuna Uku Na Gida


Rundunar sojin Najeriya ta ba jami’anta umurnin su koyi magana da harsunan Hausa, Igbo da kuma Yoruba a cikin shekara guda

Umurnin da shelkwatar sojin Najeriya ta bada akan cewa lallai jami’anta su koyi harsuna uku na kasar da suka hada da Hausa, da Inyamuranci, da Yarbanci ya zo ne a daidai lokacin da ake samun Karin dakarun dake tabbatar da tsaro a cikin gida.

Birgediya Janaral Sani Usman Kuka Sheka, ya fadi cewa Dallin bada Wannan umurnin shine don inganta yanayin aiki da kuma samun fahimtar juna. Ya kara da cewa fahimtar yare fiye da daya na cikin al’adun sojojin duniya.

Ya kuma ce wannan matakin zai ba sojoji karfin guywa akan yadda zasu fahimci sauran harsuna, musamman manyan harsunan kasar guda uku bisa la’akari da cewa zai inganta aikinsu.

Malam Abubakar Tsanni dake jagorantar wata kungiyar ‘yan kishin kasa a Najeriya, ya nuna gamsuwarsa da wannan matakin. Ya ce tabbas hakan ya nuna cewa sojojin Najeriya na da kishin kasarsu, babu ruwansu da bambancin addini ko bangaranci. Wannan zai kawo cigaba sosai a Najeriya.

Tsohon Hafsa a hukumar liken asirin sojan Najeriya, Aliko el-Rashid Haroon yace tun tuni ya kamata a dauki wannan matakin ta yadda za a kai sojojin Najeriya dake kudancin kasar arewa, na arewa kuma a kai su kudu. Ya kara da yin kira akan cewa ya kamata a kara da harshen faransanci saboda kasashen dake makwabtaka da Najeriya.

Birgediya Janaral Kuka Sheka ya ce ba a harsuna uku za a tsaya ba, kamata yayi duk inda soja ya sami kansa ya yi kokarin fahimta da koyon harshen al’ummar wurin.

Ga Karin bayani cikin sauti daga wakilin sashen hausa Hassan Maina Kaina.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG