Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Hukumar Zaben Kenya Ta Ce Uhuru Kenyatta Ne Ya Lashe Zaben Shugaban Kasa


Uhuru Kenyatta, shugaban Kenya yana tafi bayan da aka bayyanashi a matsayin wanda ya lashe zaben shugaban kasar Kenya

Hukumar zaben Kenya ta sanarda cewa shugaban kasar, Kenyatta, shi ya lashe zaben shugaban kasa duk da cewa kashi 98 cikin dari na masu jefa kuri'a sun kauracewa zaben kamar yadda madugun adawar kasar ya umurcesu

A jiya Litinin hukumar zaben kasar Kenya ta sanar da cewa shugaba Uhuru Kenyatta ne ya lashe zaben shugaban kasar da aka yi, wanda ‘yan adawa suka kauracewa da kusan kuri’u kashi 98 cikin 100.

Sai dai kuma Mutanen da suka fito zaben na ranar Alhamis, basu kai kashi 39 cikin 100 ba na mutanen da suka yi rijistar zabe su Miliyan 19 da dubu 600, a cewar shugaban hukumar zaben Wafula Chebukati.

Madugun ‘yan adawa Raila Odinga, yaki shiga zaben kuma ya kira magoya bayan sa da su kauracewa zaben, haka kuma wasu masu zanga-zaga sun hana bude runfunar zabe a wasu sassan da shi madugun ‘yan adawar ke da karfi sosai.

Zaben da aka gudanar na ranar Alhamis dai, zabe na biyu ne bayanda aka soke na farko da aka yi a watan Agustan da ya gabata wanda aka ayyana shugaba Uhuru Kenyatta a matsayin wanda ya lashe shi, amma kotun kolin kasarta watasar da shi bayanda tace ta gano an tafka magudi a cikinsa.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG