Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka Ta Dakatar da Baiwa 'Yan Turkiya Takardar Shiga Kasarta


Rex Tillerson, Sakataren Harkokin Wajen Amurka

A wata sanarwa da ofishin jakadancin Amurka dake Turkiya ya fitar ya bayyana dakatar da baiwa 'yan kasar Turkiya din takardar visa ta shiga Amurka kuma nan take ita ma kasar ta Turkiya ta mayar da martani

Amurka ta dakatar da bayar da duk wata visa ta zuwa kasar daga Turkiyya, wadda ba ta masu kaura ba, har zuwa wani lokaci, a cewar ofishin jakadancin Amurkar da ke birnin Ankara.

Wata takardar bayanin ofishin jakadancin wadda ta fito jiya Lahadi na cewa, "Wasu al'amura na baya-bayan nan sun tilasta Amurka sake nazari kan yadda gwamnatin Turkiyya ke daukar tsaron lafiyar ofishin jakadancin Amurka da kuma ma'aikatansa"

Takardar ba ta yi cikakken bayanin dalilin sake nazarin ba, da kuma ko wannan dakatarwar ta tsawon wani lokaci ce.

'Yan sa'o'i bayan nan sai Turkiyya ta mai da martani da sanarwar cewa ita ma ta dakatar da bayar da tata visa ga Amurkawa dake son zuwa kasarta, ta na mai amfani da irin lafazin da Amurka ta yi amfani da shi wajen dakatar da tata visar.

Facebook Forum

Shugaba Joe Biden ya zama Shugaban Amurka na 46

Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris

BIDIYO: Fashin baki kan rantsarda da shugaba Joseph Biden da Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:51 0:00

An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris

BIDIYO: An rantsar da sabon shugaban Amurka Joe Biden da mataimakiyarsa Kamala Harris
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46

Bikin Rantsar da Joseph R. Biden a Matsayin Shugaban Amurka na 46
please wait

No media source currently available

0:00 1:45:22 0:00
XS
SM
MD
LG