Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jordan Ta Kori Jakadan Syria


​Kasar Jordan ta kori Jakadan kasar Syria, wanda hakan ya sa ita ma Syriyar ta rama kan Jakadan kasar ta Jordan.

Wata mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Jordan ta fadi jiya Litini cewa an bai ma Jakadan Syria Bahjat Suleiman nan da sa'o'i 24 ya fice daga kasar.

A wata takardar bayanin da kafar labaran mai suna Petra ta yada, ta ce Suleiman ya yi amfani da matsayinsa a Jordan wajen kaga abin da ta kira "zarge-zarge marasa tushe" kan Kasar ta Jordan da kawayenta. Ta ce Suleiman ya yi ta cin zarafin kasar akai akai a wuraren taro, da rubuce rubuce da kuma abubuwan da ya kan saka a dandalin sada zumunci na intanet.

A wasu daga cikin abubuwan da ya saka a dandanlin sadarwar intanet, Suleiman ya caccaki kasar ta Jordan saboda ta amshi makamin cabko makamai masu linzami don magance barazanar da yakin basasar Syria ke haddasawa. Ya kuma zargi Jordan da bayar da mafaka ga sojojin Syria da su ka balle.

Nan da nan Syria ta mai da martani kan wannan shawarar da Jordan ta yanke da bayar da sanarwa jiya Litini cewa ita ma ta haramta ma karamin Jakadan Jordan da ke Dimaskus kasancewa a kasar. Jami'an Jordan sun ce jami'an diflomasiyyar ba ya ma kasar ta Syria a halin yanzu.
XS
SM
MD
LG