Malema, daya daga cikin masu sukar lamirin shugaba Jacob Zuma, ya bayyana gaban kotun dake Polokwane yau laraba a bayan da ya mika kansa ga ‘yan sanda.
A ranar jumma’ar da ta shige, hukumomi suka bayarda takardar iznin kamo Malema, kuma magoya bayansa da yawa sun kwana har zuwa yau laraba a kofar caji ofis na ‘yan sanda inda aka tsare shi.
Tuhumar da ake yi masa ta samo asali daga wasu ayyukan kwangilar da ake zargin an yi cuwa-cuwarsu a gundumar da Malema yake. Hukumomi suka ce yayi amfani da kudaden cuwa-cuwar kwangilar wajen sayen gona da wata motar alfarma.
Hudu daga cikin abokan huldarsa sun bayyana gaban kotu jiya talata dangane da tuhume-tuhume irin wannan.