Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Justice Onnoghen Ya Zama Alkalin Alkalan Najeriya


 Chief Justice Onnoghen sabon alkalin alkalan Najeriya
Chief Justice Onnoghen sabon alkalin alkalan Najeriya

Daga yau 7 ga watan Maris na shekarar 2017 Babban Alkali Walter Onnoghen ya zama alkalin alkalan Najeriya bisa ga rantsar dashi da Mukaddashin Shugaban kasa Farfasa Osinbajo yayi

Mai girma alkalin babban kotun kolin Najeriya ya zama ubangida kuma bango majinginin abun tinkahon jama'a, mai daidaito da tabbatar da adalci da gaskiya, inji Mukaddashin Shugaban kasa Farfasa Osinbajo.

Farfasa Yemi Osinbajo wanda yayi magana cikin sassauyar murya da ban tausayi yaci gaba da cewa zama alkalin alkalan kasa wani babban nauyi ne da ya maida dan Adama tamkar Ubangij Allah Madaukakin Sarki. Ya gayawa alkalin cewa yana da iko kan rayuwa na mutane baki daya. Kana da ikon tabbatar da mulkin mai mulki ko kuma ka fitar dashi daga mulki.Kana da ikon sa ido akan duk alkalai, inji Farfasa Osinbajo.

Bayan an rantsar dashi sabon alkalin alkalan Walter Onnoghen yace ya tabbatarwa al'ummar kasar zaman lafiya ta hanyar aikata gaskiya da adalci a harkokin shari'a.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:06 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG