Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalaman Gwamnan Benue Kan Makiyaya Ya Janyo Suka Daga Kungiyoyi


Gwamnan Benue Samuel Ortom.
Gwamnan Benue Samuel Ortom.

Kalaman gwamnan jihar Benue mai cewa fadar shugaban kasa na rikon sakainar kashi kan irin kashe-kashen da ake zargin Fulani makiyaya da aikatawa a sassa daban-daban na Najeriya, ya janyo kakkausan martani daga wasu kungiyoyi dake hankoron samar da ci gaban Najeriya.

A wani jawabi da ya yi wa manema labarai, gwamnan jihar Benue, Samuel Ortom, ya bukaci gwamanatin tarayya da ta fito fili ta kalubalanci, tare kuma da kama, makiyayan dake daukar bindigogi kirar AK47.

Sai dai wasu kungiyoyi uku masu goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari, sun maida martani kan kalaman na Ortom, ta hanyar fitar da wata takardar hadin gwiwa, inda suka bayyana shugaba Buhari a matsayin mutum na gari dake yin adalci ga kowa.

Shugaban kungiyar Fulani ta Miyetti Allah ta kasa, Muhammadu Kiruwa ya ce irin abubuwan da ake wa Fulani a kasar sun wuce hankalin mutum guda. Idan ana tuhumar mutum da aikata laifi bincike ya Kamata a gudanar ba wai kira da a kama mutum ba.

Mai fashin baki kan lamura, Yakubu Gidado ya ce samun adalan shugabanni ne kawai zai kawo karshe rashin tsaro da Najeriya ke fuskanta.

Domin cikakken bayani saurari rahotan Zainab Babaji.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00

Karin bayani akan: Jihar Benue, Samuel Ortom, Nigeria, da Najeriya.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG