WASHINGTON DC —
A shirin na wannan makon, batun wata ma’aikaciyar gwamnati da ke aikin asibiti ne da ta rungumi sana’ar saida kunun aya da ya habaka a birnin tarayya Abuja da kewaye.
Mun kuma haska fitila kan wata dabi’a da ke ciwa mata da dama tuwa a kwarya, inda ake samun wadansu suna auren mazan abokansu ko dai a matsayin kishiyoyi ko kuma su yi sanadin mutuwar auren kawar su auri mazansu.
Saurari shirin:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.
Dandalin Mu Tattauna