Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru: An Kama Wasu Ɗalibai Yan Makarantun Sakandare Da Laifin Dillancin Karuwai


Yan sanda suna binkicen wasu matasa.

An kulle wadansu matasa maza 9 da mata 5 daliban makarantar sakandare da aka kama da laifin dillancin karuwai a makarantu, a babban gidan yari na birnin Kribi .

Wadannan dalibai 14, masu shekaru 13 zuwa 16, ana zarginsu da fyade, dillancin karuwai da kuma shan kwayoyi.

Wasu matasa masu shan kwaya
Wasu matasa masu shan kwaya

Bayan korafe-korafen iyaye da suka gano ‘ya’yansu suna dauke da dabi'un da ba su dace ba. An gano munanar ayyukansu din bayan rashin cika alkawari a tsakaninsu

Wasu dalibai maza sun bukaci lalata da kawayen karatunsu mata biyu kamar yadda suka saba. Kuma suka yi bidiyo suka yada a kafafen sada zumunta. Anyi haka ne bayan alkawarin bai wa kowace daga cikin matan jaka arba'in (40 000 F) na kudin CFA.

Rashin cika wannan alkawarin ne yasa yaran mantan suka kai kara wajen babban mai kula da su. Bayan bincike na cikin gida, shugaban makarantar ya kira taron majalisar ladabtarwa ta musamman.

Daga baya ne ya daukaka kara gurin alkalin da ya ba da umarni a zurfafa bincike. Wanda zai kai ga gane cewa, kungiya ce musamman take kafe don wadannan aika aika a cikin makarantu.

Musa Ousseini, shugaban kungiyar farar hula kuma mai kula da tarbiyar matasa yace lamarin abun mamaki ne kuma dole a tashi tsaye a dakile wannan dabi’o’I na batsa.

Binciken kuma ya baiwa wasu daga cikin daliban damar yin cikakken bayani. Sun bayyana cewa sun kasance karƙashin rinjayar wasu manya, wadanda suke shugabantar wannan kungiyar dillancin.

A cewar mai gabatar da kara, binciken da ake ci gaba da gudanarwa, zai ba da damar cafke daukacin shugabannin kungiyar da mabiyansu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00

Dubi ra’ayoyi

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG