Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Jiragen Sama Na Arik Ya Shigar da Kara kan Yunkurin Sayarda Shi


Jirgin kamfanin Arik na jigilar fasinja na Najeriya.
Jirgin kamfanin Arik na jigilar fasinja na Najeriya.

Lauyoyin kamfanin Arik sun shigar da kara kotu suna kalubalantar yunkurin sayar da kamfanin wa kamfanin jiragen sama na kasar Habasha.

Karar da lauyan kamfanin na Arik Babatunde Koko da wasu lauyoyin suka shigar a gaban wani kotun Legas suna neman kotun ta hana ma'aikatar sufuri ta tarayya da kamfanin Ethiopia Airline da cigaba da duk wata tattaunawa da zata kaiga mallakawa kamfanin Ethiopian kamfanin Arik din.

Kamfanin na Arik na kukan cewa tun bayan da kamfanin gwamnati mai kula da kadarori da aka sani da suna AMCON ya kwace shi ranar 8 ga watan Fabrarirun wannan shekarar kamfanin Arik din ya shigar da kara domin kalubalantar matakin.

Lauyoyin na mai cewa yayinda suke da kara a kotu basu ga dalilin da zai sa kamfanin Ethiopia ya fitar da sanarwar tattaunawa da gwamnati kan kokarin mallakar kamfani Arik ba.

A wani bangaren kuma kamfanin na Arik ya bukaci Antoni Janar kuma ministan shari'ar Najeriya da ya gudanar da bincike akan kamfanin na Ethiopia bisa zargin cewa kamfanin ya kawo tsaiko a harkokin shari'ar Najeriya.

Alhaji Usman Kofar Kudu masani kan harkokin zirga zirgan jiragen sama yace idan akwai tattaunawa tsakanin gwamnati da wani kamfanin jiragen sama yakamata a ce duk kamfanonin da abun ya shafa suna da masaniya kuma tare dasu za'a tsayar da shawara.

Yanzu da harkokin Arik sun fara farfadowa bai kamata a ce sun koma karkashin wani kamfanin ba, inji Alhaji Usman.

Alhaji Abdullahi Abuja ya kira bangarorin su zauna su sasanta saboda tattalin arziki ba ya cigaba ba tare da 'yan kasuwa ba masu zaman kansu.

Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:34 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG