Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin NNPC Ya Shigo da Man Jirgin Sama Kimanin Lita Miliyan 38


Jiragen sama
Jiragen sama

Biyo bayan karancin man fetur na jiragen sama da ake fama dashi a Najeriya kamfanin man fetur na kasar wato NNPC ya shigo da lita miliyan 38 da 'yan kai domin shawo matsalar da ta addabi zirga zirgan jirage cikin kasar

Rahotani sun nuna wasu jiragen da kan shiga Najeriya sai sun biya ta kasar Ghana su sha mai kafin su cigaba da tafiyarsu.

Jami'in labaru na kamfanin NNPC shi ya bayyana matakin da kamfanin ya dauka domin rage kalubalen da ake fuskanta a daidai lokacin da ake zirga zirgan karshen shekara da ya hada da bikin kirsimati da sabuwar shekara.

Yayinda yake jajinta kalubalen da kan haddasa cunkoso a filayen jirage da ma soke tashin jiragen na cikin gida da na ketare ministan zirga zirgan jiragen saman Najeriya Hadi Sirika yace damuwar ta wucin gadi ce.

Yace sun nunawa kamfanin NNPC mahimmancin fara yin man a Najeriya domin da can ana yi a Kaduna da Fatakwal. Kamfanin yayi alkawarin zasu fara yi kwana kwanan nan. Baicin hakan sun je babban bankin Najeriya da ma'akatar kudi cewa ya kamata a ba ma'aikatar jiragen sama mahimmanci a samo dalar Amurka domin a shigo da man.

Bayan wadannan Hadi Sirika yace sun lallashi masu hannu da shuni kaman kamfanin MRS da Sahara suka rokesu su shigo da man domin a samu masalaha.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:41 0:00

XS
SM
MD
LG