Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Twitter Ya Ninka Adadin Harufa daga 140 Zuwa 280


 Twitter
Twitter

A wani labari da ake hasashen zai yi wa shugaban Amurka Donald Trump dadi, kamfamin Twitter ya ninka adadin haruffan da yake ba da dama masu amfani da shi su rika yin rubutu domin aika sakon kar-ta-kwana, ko kuma text message.

Kamfanin na Twitter ya kara adadin haruffan ne daga 140 zuwa 280.

Sai dai duk da cewa shugaba Trump ya mayar da shafin na Twitter wani muhimmin tambari, kamfanin ya ce daruruwan miliyoyin masu amfani da shafin, ba sa cin cikakkiyar gajiyarsa wajen amfani da shafin domin su aika da sako.

Kamfanin na Twitter ya ce, yana fatan kara adadin haruffan da ya yi zai sa mutane su raja’a wajen amfanin shi wajen aikawa da sako.

“Muna so ne ya zamanto abu mai sauki da kuma sauri, domin jama’a su bayyana abinda ke zukatansu.” In ji kamfanin na Twitter.

A watan Satumban da ya gabata, kamfanin ya fara gwaji kan fadada shafin, lamarin da ya samu karbuwa daga masu amfani da shi.

Nan gaba ana sa ran kamfanin na Twitter, zai sake fadada shafinsa domin rungumar wasu karin harsuna, amma ban da harshen China da Japanese da kuma Korea, saboda karancin kalmomin da suke amfani da su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG