Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanonin Mai Da Iskar Gas 51 Suna Bin Gwamnatin Najeriya Bashin Naira Tiriliyan 1.32-Neiti


.

Hukumar kula da kudaden shigar da ake samu a man fetur da iskar gas da kuma ma’adinai a Najeriya tafitar da wani rahoto akan bincikenta na shekarar 2020.

ABUJA, NIGERIA - Rahoton ya gano cewa kamfanonin mai da iskar gas guda 51 ne ke bin gwamnatin tarayya bashin sama da dala biliyan uku a shekarar 2020, batun da ya aza ayar tambaya kan an karkatar da kudaden ne daga asusun gwamnati.

Rahoton na hukumar ta NEITI na shekarar 2020 ya bayyana cewa Najeriya ta samu dala biliyan 20.43 daga bangaren mai da iskar gas a shekarar, adadin da ya nuna an samu raguwar kashi 40% idan aka kwatanta da dala biliyan 34.22 da aka samu daga fannin a shekarar 2019.

Malam Sa’ad Balarabe shi ne mataimakin darakta a hukumar kula da kudaden shigar da ake samu a man fetur da iskar gas da kuma ma’adinai a Najeriya NEITI ya yi wannan bayanin.

Rahoton ya kuma kara da cewa, yawan kamfanonin da suka kasa biyan bashin ya ragu daga 77 wadanda hukumar ta ruwaito a shekarar 2019 zuwa 51 a shekarar 2020.

Kamfanin kula da albarkatun man fetur na Najeriyar NNPC da ke da kyakyawan alaka da hukumar ta Neiti ta bakin babban jami’in kula da harkokin kudade na kamfanin Malam Umar Ajiya ya bayyana cewa sun himmatu wajen samar da bayanai ga al’umma da kuma inganta ayyukansu a kasar.

Wannan dai shi ne karo na 13 da hukumar NEITI tare da hadin gwiwar hukumar EITI ke fitar da irin wannan rahoto, kuma ya zuwa yanzu rahoton ya binciko biyan kuɗade haraji daga hukumomi guda tamanin da uku wadanda suka hada da kamfanonin mai da iskar gas guda sittin da tara da hukumomin gwamnati goma sha uku da kuma kamfanin iskar gas na Najeriya wato NLNG a takaice.

Saurari rahoto cikin sauti daga Shamsiyya Hamza Ibrahim:

Rahoton Binciken Neiti Ya Ce Kamfanonin Mai Da Iskar Gas 51 Suna Bin Gwamnatin Najeriya Bashin Naira Tiriliyan 1.32
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:37 0:00

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG