Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kankara Ta Fado Daga Sama A Lokacin Zafi


Lima orang tahanan duduk di atas atap salah satu bangunan di Pusat Penahanan Villawood di Sydney, Kamis (21/4).
Lima orang tahanan duduk di atas atap salah satu bangunan di Pusat Penahanan Villawood di Sydney, Kamis (21/4).

Wata mulmuleliyar kankara da girman ta yakai girman kwallon kafa ta fado kan rufin wani gida daga sama, ana dai kyautata zaton ta fado ne daga jikin wani jirgin sama da ya wuce ta kan gidan.

Matar gidan mai suna Monica Savath tace ita da sauran iyalin gidan suna zaune a babban ‘dakin gidan alokacin da suka ji fadowar wani abu kan gidansu, tace karan dai yayi kamar fashewar bom, sun dai ruga da gudu zuwa garejin gidan inda suka tarar da rufin gidan ya bule da kuma barbadin kankara ko ina, Allah dai ya kiyaye babu wanda ya raunata.

Jim Mathews wani masani kan harkar yanayi, ya watsar da duk wani bayani na kimiyya dan gane da inda ake tsammanin wannan kankara ta samo asali a irin wannan lokacin da ake fama da tsananin zafi. A tunanin sa jirgin sama ne kadai zai iya haddasa faruwar wannan lamari.

XS
SM
MD
LG