Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

KANO: An Kammala Taron Fahimtar Harkokin Addini da Siyasa


Taron kasa da kasa kan addini da siyasa bisa koyaswar marigayi Hassan al-Turabi
Taron kasa da kasa kan addini da siyasa bisa koyaswar marigayi Hassan al-Turabi

An kammala taron kasa da kasa akan koyarwa da fahimtar harkokin addini da siyasa na marigayi Dr Hassan AL-Turabi, wanda a shekarun baya-bayan nan ya jagoranci kawo sauyi kan lamuran addini da siyasa a kasar Sudan da sauran sassan duniya.

Bayan nazari da mahawara akan makaloli 19 da shehunan malamai daga Jami’o’i da cibiyoyin binciken harkokin ilimi na ciki da wajen Najeriya, mahalarta taron sun gabatar da kudurori da dama wadanda ke kunshe cikin takardar bayan taro da aka fitar a zauren taro na tsangayar nazarin aikin lauya ta Jami’ar Bayero, Kano.

Dr Kabiru Haruna Isa, yace shawara ta farko ita ce a ci gaba da yin irin taron domin masana su zo su tattauna su yi nazari akan matsalolin al’umma su kawo ainihin mafita.

An kuma bada shawarar cewa harkar ilimin mata a bashi mahimmanci da abubuwan da suka shafi harkokin iyali da matsalolin damunsu. Ya kamata a kallesu da idon basira

Sannan an bada shawarwari akan matsalolin bara a cikin al’umma da kuma matsalolin dangantaka tsakanin addinai

Wani mutum mai sunaAliyu Muhammad ya ce taron ya zaburar dasu akan abubuwan da suka shafi addini da siyasa. Shi ma Ahmad Rashid Makarfi y ace ya koyi mahimmancin zaman lafiya akan cewa duk wani shugaba wajibi ne ya hada kan jama’arsa ya tabbtar da zaman lafiya

Dr Umaimah Al-Turabi na daga cikin ‘yayan magayi Sheikh Hassan Al-Turabi ya Haifa, wadda ta baiyana farin ciki da taron da aka yi akan ayyukan mahaifnta

A karshen dai wadanda suka shirya wannan taro sun sha alwashin mika abubuwan da aka cimma ga hukumomi da sauran masu ruwa da tsaki domin dubawa.

A saurari rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG