Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kara Kaimi Kan Ilimin Injiniya Shi Zai Kaiga Samun Galaba Kan Dabarun Fasaha


Fasahar aikin Injiniya
Fasahar aikin Injiniya

Ya zama wajibi Najeriya ta kara kaimi kan ilimin ijiniya da hakan zata samu galaba kan dabarun fasaha wanda zai zama mabudin tattalin arziki

Sabon shugaban ijiniyoyin Najeriya Ademola Isaac Olorunfemi ya ce idan har Najeriya na son cigaba ta kuma habbaka tattalin arzikinta to ya zama wajibi ta kara kaimi kan ilimin injiniya domin ta samu galaba kan dabarun fasaha

Yayin da yake jawabi wurin gagarumin bikin baza kolin fasahan injinoyoyin Najeriya yana ganin suna daidai da yin kunnen doki da wasu injiniyoyin duniya idan ma basu wuce wasu ba, ciki ma har da masu cigaban masana'antu. Taron tamkar na share faggen karbar taron ijiniyoyin duniya ne da za'a yi a Najeriya bana. Cikin jawabinsa ya yi bankwana da tsohon shugaban kungiyar injiniyoyin Najeriya Mustapha Balarabe Shehu mai barin gado. Shi Injiniya Balarabe Shehu yana jiran gadon zama shugaban ijiniyoyin Afirka gaba daya.

Injiniya Shehu ya ce zasu matsa kaimi wajen horas da injiniyoyin Najeriya domin cigaba da tafiya daidai da zamani. Ya ce zasu tabbatar an horas da injiniyoyi kan sabbin abubuwa dake fitowa da kuma sabbin kalubale da gwamnatoci ke fitowa dasu. Ya ce dalili kenan da ya sa suna da cibiyoyin koyas da injiniyoyi kan fannoni iri-iri. Akwaisu a Legas da Abuja da Fatakwal. Nan ba da dadewa ba za'a bude wata a Kano da kuma wata a Gombe. Burinsu shi ne a duk yankunan Najeriya shida sun bude cibiyoyin koyaswa saboda injiniyoyi koina a Najeriya su samu wurin zuwa domin samun horaswa a bangarori iri-iri.

Ijiniya Shehu Hadi Ahmed wanda ya samu lambar yabo ya yi alwashin Najeriya zata fara kire-kiren naurorin da yanzu shigo dasu ake yi. Ya ce an fara da hada motoci a Najeriya amma burin shi ne ta wannan hanyar zasu yi anfani da albarkatun karafan da Allah ya ba kasar Najeriya su fara kira nasu.

To sai da wasu sun ce akwai kwararrun injiniyoyi a Najeriya amma rashin lantarki da rashin kyakyawan yanayi da tallafawa masu fasahar kere-kere kan kawo cikas wajen cin gajiyar ilimin injiniyoyin.

Ga rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:16 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG