Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karamar Hukumar Bosso ta sayar da shanun sata


Kungiyar makiyaya ta Miyatti Allah dake tarayyar Najeriya, ta nuna damuwa game da matakin da karamar hukumar Bosso ta dauka, na sayar da wadansu shanun sata da aka bata ajiya.

‘Yan sanda sun mikawa karamar hukumar ajiyar shanun ne bayan sun kwato su daga hannun barayi. Hukumomin karamar hukumar sun bayyana cewa, lalurar rashin lafiya ne yasa suka kai shannun kasuwa.

A cikin hira da Muryar Amurka shugaban kungiyar miyatti Allah na jihar Naija Hardo Adamu Kaduna yace kimanin shanu dari ne aka sace masu a jihar Naija, kuma kawo yanzu ko guda daya ba a mayar masu ba. Bisa ga cewarsa, hukumomin karamar hukumar sun shaida masu sun sayar da wadansu shannun yayinda suka tura keyarsu zuwa asibitin dabbobi inda suka ce ana yiwa sauran shannun jinya.

Wadansu makiyayan da Sashen Hausa ya yi hira dasu sun ce sun ga shanunsu a kasuwa inda aka kai domin saidawa, yayinda suka kuma bayyana cewa, ba a basu koda anini ba na kudin da aka ce an sayar da sauran shanun.

Da yake maida martini, Alhaji Garba Yarima mataimakin shugaban karamar hukumar Bosso, kuma shugaban kwamitin kula da shanun ya tabbatar da kai shanu uku kasuwa da yace basu da lafiya, da nufin sayar da su ayi jinyar sauran da yace basu da lafiya. Sai dai bai bayyana adadin shanun da aka basu ajiya ba.

Ga cikakken rahoton da wakilin Sashen Hausa Mustapha Nasiru Batsari ya aiko daga Minna, Jihar Naija Najeriya.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG