Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Bayani kan Harin da Aka Kai Nijar


Wasu Jami'an Tsaron Nijar

An samu karin bayani daga hukumomin Nijar dake arewacin kasar kan harin da aka kai wanda yayi sanadiyar mutuwar mutane hudu.

Hukumomi daga arewacin Jamhuriyar Nijar sun yi karin bayani game da harin da aka kaiwa kasar ranar Asabar da ta gabata a lokacin da wasu mutane da ba'a tantance ba suka farma jami'an tsaro dake yawon sintiri

Harin ya haddasa rasuwar mutane hudu kamar yadda shugaban gundumar ya shaidawa manema labaru. Alhaji Nafalla yana mai cewa wata mota ce akorikura kirar toyota mai launin ruwan toka ta zo daidai da inda jami'an tsaro suke ta bude masu wuta.

Nan take mutane uku suka mutu, biyu suka jikata amma na hudun ya cika ne a asibiti.

Harin an kai ne a gap da garin Asamaka dake kan iyaka da kasar Algeria. Bayan harin jami'an tsaro sun bada umurnin a bi sawun maharan har cikin kasar Algeria domin a farautosu.

Jami'an basu ga kowa ba amma ana cigaba da daukan tsauraran matakai da hukuma ba zata iya bayyanawa 'yan jarida ba.

Ga rahoton Haruna Bako da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:02 0:00

Facebook Forum

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG