Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Kudin Shiga Jirgin Kasa Ya Janyo Ce-ce-ku-ce a Najeriya


Fasinjoji na fitowa daga jirgin

Gabanin rufe tashar jiragen sama ta Abuja domin gyara, ya sa gwamnati ta gina hanyar layin dogo na zamani tsakanin Abuja da Kaduna tare da samar da taragun zamani lamarin da ya sa fasinja ke balugor cikin sauki tskanin biranen biyu.

Amma wani abun da ya jawo ce-ce-ku-ce yanzu shi ne karin kudin shiga jirgin da mahukunta suka yi bayan dan lokaci kadan da fara aiki.

Da farko da aka fara ana biyan N600 a bangaren yaku-bayi kana manyan mutane na biyan N900.

Yanzu na N600 ya haura zuwa N1050 yayin da na manyan mutane ya haura zuwa N1500.

Tsarin jirgin kasa daga Abuja zuwa Kaduna yana samun yabo daga wadanda suke shiga jirgin saboda sun nuna jin dadinsu.

Victor Adamu shugaban sashen aikace-aikace na tashar jirgin ya ce karin kudin shiga jirgin ya zama masu dole ne saboda duk abubuwan da suke bukata domin jirgin ya yi tafiya basa samunsu da sauki dalili ke nan da ya sa suka kaiwa gwamnati kokensu aka amince masu su yi karin.

Wata fasinja mai suna Usaina Maimunatu Ali ta ce wasu ba za su iya shiga jirgin ba saboda karin da aka yi.

Amma wata cewa ta yi duk karin da zai kai ga biyan bukata ba shi da matsala.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:38 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG