Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Kumallo Ne Ke Sani Makara Zuwa Gurin Aiki Na


A teacher conducts a mathematics lesson to high school students in Democratic Republic of Congo town of Bunagana, Oct. 19, 2012.
A teacher conducts a mathematics lesson to high school students in Democratic Republic of Congo town of Bunagana, Oct. 19, 2012.

Wani malamin makarantar firamare mai suna Anderson Roosevelt a Jihar New Jersey, ya makara zuwa gurin aikin sa har sau 111 cikin shekaru biyu, akoda yaushe aka tambayeshi dalilin sa na zuwa a makare sai yace ya tsaya karyawa ne ya makara.

Kasancewar hukumar makarantar ba zata iya korar malamin ba har sai tabi ta gurin mai shiga tsakani, inda mai shiga tsakanin yaki korar Anderson kan wannan laifi na yawan makara, har ma yake cewa kamata yayi a hukunta malamin a baya lokutan da yake laifin ba sai yanzu ba a hada laifukan kuma ace za’a koreshi.

Yanzu haka dai an tura wannan malami hutun dole ba tare da biyan sa ko sisi ba, har sai zuwa 1 ga watan Janairu na shekara mai zuwa kafin ya dawo bakin aiki.

Alokacin da yake magana da kamfanin dillancin labarai na Associated Press jiya Juma’a yace a duk lokacin da ya makara, yanayi ne dalili karyawa da yake batare da lura da lokaci ba.

Ya bayyana yadda wannan dabi’a ta janyo masa rashin samun albashin sa, amma ya godewa Allah da ba’a iya korar sa ba yakuma yi aniyar zuwa aiki kan lokaci bayan ya koma.

XS
SM
MD
LG