Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karya Darajar Naira Tamkar Kashe Najeriya Ne Inji Shugaba Buhari


Shugaban Najeriya, Muhammadu Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya fadi cewa ba zai karya darajar naira ba saboda a ganinsa karya darajar kudin na Najeriya kamar karya kasar ne.

Buhari ya bayyana haka ne a ga ‘yan Najeriya a kasar Kenya da ya kai ziyara. Ya fadi cewa, karya Naira ba abinda zai ja wa talakan Najeriya sai karin azabar rayuwar da a yanzu suke fuskanta sakamakon nakasashshen tsarin tattalin arziki da aka bi a baya.

Ya kara da cewa, gwamantocin baya sun bi rarraunar hanyar da bata dace da rauywawar talakawa ba ta yadda za su amfana daga dimbin arzikin da Allah ya yiwa giwar nahiyar Afirka din. Shugaban ya ce in har zai yarda da karya darajar Naira, to kuwa masana tattalin arziki na da jan aikin samun amincewarsa.

Inda yake bayyana musu cewa sai an yi masa bayanin gamsashshe kuma mai cike da hujjojin yin hakan. Wani masanin tattalin arziki Malam Sani Aminu Dutsin-Ma, ya bayyanawa Wakilinmu Umar Faruk Musa cewa, wannan shawara ta Buhari abar dubawa ce.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Sakataren Gwamnatin kasar Amurka Michael R. Pompeo

Magoya Bayan Trump Sun Afkawa Ginin Majalisun Amurka

Magoya Bayan Shugaba Donald Trump Sun Mamaye Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:56 0:00

Rayuwar Birni

Rayuwar Birni: Hira da Aliyu Danlami mai sayar da furanni a Abuja
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:49 0:00
Karin bayani akan Rayuwar Birni
XS
SM
MD
LG