Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Afirka ta Kudu Na Shirin Ficewa daga Kotun Manyan Laifuka Na Dunia ko ICC


Alkalan kotun kasa da kasa da lauyoyi

Kasar Afirka ta kudu tace zata fita daga Kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya da ake kira ICC.

A yau juma’a ne Ministan Shari’a Michael Musuthu ya bayyana cewa za a mikawa majalisar dokokin kasar kudurin dokar da zata nemi Afirka ta Kudu ta soke hannun da kasar ta rattaba a kan Yarjejeniyar Roma da ta kafa wannan kotun.

Yarjejeniyar ta tanadi cewa tilas ne bisa shari'a duk kasar da ta sanya hannu kanta, ta kama duk wani wanda kotun ke nema. An kafa kotun bin kadin manyan laifuffuka ta duniya da zummar hukumta masu aikata kisan kare dangi, laifuffukan yaki da kuma na cin zarafin bil Adama.

Amma kuma kasashen Afirka sun bayyana cewa kotun ta maida hankali ne kadai akan shuwagabannin nahiyar.

Ficewar Afirka ta Kudu daga kotun ta ICC ta samo asali ne tun lokacin wata ziyarar da Shugaban Kasar Sudan Omar Al-Bashir, ya kai kasar bara domin halartar taron kolin kwanaki biyu na Kungiyar Tarayyar Afirka.

Yayin da wata kotun Afirka ta Kudu din ke bin bahasin ko ta bada umurnin a kama shi, shugaba Bashir yayi watsi da umurnin kotun da ta ce ya tsaya a kasar, ya koma kasarsa inda hukumomin Afirka ta Kudun ba zasu iya taba shi ba.

Jami'an Afirka ta Kudu sun ce shugaba Bashir yana da kariyar diflomasiyya a matsayinsa na shugaban kasa da kuma zama wakili mai halartar taron kolin Kungiyar Tarayyar Afirka a Johannesburg.

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG