Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Dimokradiyar Kwango Ba Zata Halarci Taron Neman Mata Tallafi Ba


Shugaban Democratic Republic of Congo Joseph Kabila
Shugaban Democratic Republic of Congo Joseph Kabila

Mahukuntan kasar Dimokradiyar Kwango sun ki amincewa da halartar taron neman wa kasar tallafi da Majalisar Dinkin Duniya ta shirya bisa abun da ta kira wani yunkurin cin mutuncin kasar

Yayinda masu bada tallafi ko gudumawa na kasa da kasa suke shirin zasu hallara yau jumma'a a birnin Geneva, domin yin wani babban taron neman gudumawa da Majalisar Dinkin Duniya, MDD, ta shirya domin agazawa kasar Jamhuriyar Demokuradiyyar Kwango, gwamnatin wannan kasa dake yankin Afirka ta tsakiya, wacce Allah Ya yiwa albarkatun ma'adinai tana kan bakarta cewa ba zata halarci taron ko ta bada hadin kai kan taron ba. Wakiliyar Muryar Amurka Anita Powell, ce ta aiko mana da wannan rahoto daga Johannesburg.

MDD tace fiye da yara miliyan biyu suke fuskantar barazanar mutuwa saboda matsanancin rashin kayayyakin abincin gina jiki.

Wani mai baiwa shugaban kasar shawara Patrick Nkanga, ya gayawa MA cewa, gwamnati bata amince da yadda aka shirya taron neman gudumawar ba, kuma tilas ne a mutunta diyaucin kasar.

Ya kara da cewa dagan-gan wadanda suka shirya taron suka gabatar da yanayin da kasar take ciki da nufin zubda mutuncin kasar. Ya ci gaba da cewa an gaza cika sharuddan da gwamnatin kasar ta gindaya domin taron. Mr. Nkanga ya ce baki daya makasudin taron kamar yadda wadanda suka shirya taron suka gabatar bai yi dai dai da har gwamnatin kasar zata bada hadin kanta ba.

Sai dai majami'ar Catholika a kasar bata goyi bayan gwamnatin kan kin halartar taron ba. Har aka ji wani babba a darikar a birnin Kinshasa yana gayawa mabiya cocin a ranar Lahadi cewa, "ba zamu ki agaji ba yayinda muke zaune hannu banza bamu da komai."

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG