Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Jamus Zata Kafa Wani Sansanin Sojoji A Kasar Nijar


Shugabar Kasar Jamus Angela Merkel

A yayin bikin cika shekaru ishirin da shida da dunkulewar gabashi da yammacin Jamus zama kasa daya, jakadan kasar ta Jamus a Jamhuriyar Nijar Dr. Paul ya bayyana anniyar kasarsa na kafa sansanin sojojinta a Nijar da zummar taimakawa dakarun Majalisar Dinkin Duniya dake kiyaye zaman lafiya a Mali

Jamus zata kafa rundunar sojojin nata ne a birnin Yamai da zummar kara karfafa sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ko MDD dake kasar Mali.

Wannan matakin na Jamus ya kara jaddada irin dangantakar dake akwai tsakaninta da kasar Nijar inji jakadan na Jamus.

To saidai tuni masu sharhi akan alamuran yau da kullum suka fara bayyana ra'ayoyinsu akan wannan anniyar ta kasar Jamus. Alhaji Salisu Ahmadu wani kusa a kungiyar dake kishin kasa mai adawa da kafa sansanin sojin wata kasa a Nijar yace yakamata kasar tayi takatsantsan. Yace turawan sun san abun da suke so, Nijar ce bata san abun da take so ba. Jamus zata yi anfani da kasar Nijar ce kawai ta ci riba.

Domin jin karin bayani daga bangaren gwamnatin Nijar kakakin gwamnatin Asmaila Malam Isa ya ki yace komi domin a cewarsa batu ne da ya shafi tsaro. Shi ma ministan tsaro da aka tuntubeshi yace yana cikin wani taro.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

Bidiyo

Mijin Aljana A Kano: Shin Dama Aljanu Na Da ATM’ Na Kudi?
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Yadda Aka Kashe Sojojin Najeriya 11 A Jihar Benue Da Ke Arewacin Kasar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG