Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Jordan Ta Cika Alkawarin Da Tayi Wa Nigeria


NIGERIA: Janara Mansur Dan Ali Ministan Tsaro
NIGERIA: Janara Mansur Dan Ali Ministan Tsaro

Kasar Jordan na daya daga cikin kasashen da tayi wa Nigeria alkawarin bata makamai, yanzu haka dai ta cika wannan alkawarin, saura kasar Saudi Arabia ita ma ta cika nata.Ministan Tsaron Nigeria Janar Mansir Dan Ali yayi wannan albishir din a zantawar su da Sarfilu Hashim Gumel.

Ministan tsaron Nigeria, Janar Mansir Dan Ali mai ritaya ya bayyana jawabin shugaba Muhammadu Buhari a zauren majilisar Dinkin Duniya a matsayin tamkar na shugaban Afrika, ba Nigeria kadai ba.

Ministan yana magana ne a lokacin da suke tattaunawa da wakilin Sashen Hausa Sarfilu Hashim Gumel a birnin New York, lokacin taron Majilisar Dinkin Duniya.

Yace hatta Sakataren majilisar Dinkin Duniya ya yaba da jawabin na shugaba Muhammadu Buhari domin yadda ya nuna cewa shi shugaba ne na Afrika ba ma Nigeria ba, musammam akan batutuwa irin su gwagwarmayar da Koriya ta Arewa keyi da sauran kasashen duniya.

Haka kuma Ministan ya tabo muhimmancin ziyarar da ‘yan kwanan kwamitin sulhu na Majilisar suka kai kasashe hudu dake makwabtaka da Nigeria masu fama da ‘yan ta’adan Boko Haram.

General Dan Ali kuma yay aba da gudunmowar makamai da kasar Jordan ta baiwa Nigeria, inda ya tabattarda da cewa ba shakka ta basu jiragen yaki da wasu kayayyakin tsaro don cika alkawarin da tayi wani lokaci can baya.

Ga Sarfilu Hashim da cikkakiyar hirar da suka yi da Ministan Tsaron na Nigeria:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG