Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bayan fatattakar 'yan Boko Haram da Najeriya ta ce ta yi daga dajin Sambisa, ita ma kasar Kamaru ta zayyana jerin nasarorin da ta ce ta yi a yaki da mayakan. Wannan na zuwa a daidai lokacin da Janhuriyar Nijar ma ke sassauta matakan tsaro a yankin Diffa saboda saukin da aka dan samu.

Kakakin gwamnatin Janhuriyar Kamaru wanda shi ne kuma Ministan Sadarwar kasar, Isa Ciroma Bakari ya yi ma manema labarai jawabi a ofishinsa da ke birnin Yaoundé kan irin nasarorin da sojojin kasar ke samu a yaki da Boko Haram musamman a jahar Arewa Mai Nisa. Ya ce an fi fafatawar ce a wajejen kan iyakokin Najeriya da Chadi.

Ministan ya ce a ‘yan kwanakin nan sojojin Kamaru sun hallaka mayakan Boko Haram sama da 100, banda manyan makamai da motoci da kuma wayoyin salularsu da sauran kayan hada bama-bamai da su ka kwato. Ya ce su kuma ‘yan Boko Haram din sun kashe sojoji uku. Ministan ya ce ko a jiyan nan sai da wasu ‘yan mata ‘yan kunar bakin wake su hudu su ka tarwatsa kansu a wajejen kan iyakar Najeriya su ka raunata wasu ‘yan banga uku, wadanda aka garzaya da su asibiti.

Wakilinmu a Kamaru wanda ya aiko da rahoton, Awal Garba, ya yi hira da wani dan yankin Marwa mai suna Malam Abubakar kan yadda su ke ganin yanayin tsaro a yankin nasu sai ya ce gwamnatin Kamaru na ba da himma sosai wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin na Marwa.

Ga Muhammad Awwal Garba da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00

XS
SM
MD
LG