Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Sudan Ta Kame Wasu 'Yan Jarida


(File) Journalists report from outside the former South African President Nelson Mandela's house, in Johannesburg, South Africa Monday, Sept. 2, 2013.
(File) Journalists report from outside the former South African President Nelson Mandela's house, in Johannesburg, South Africa Monday, Sept. 2, 2013.

Kasar Sudan ta rike wasu 'Yan jarida domin binciken su akan rahoton karin farashin kayayyakinmasarufi da ya haifar da zanga-zanga.

Amurka tayi ALLAH waddarai da kulle wasu ‘yan jarida dake aiki da kamfanin Dillacin Labarai na kasar Faransa da kuma dama na Reuters.

Kasar Sudan ce dai tayi hakan lokacin da ‘yan jaridar ke daukar rahoton wani zanga-zanga a ranar jumaa.

Maaikatar harkokin wajen Amurka tace tana sane da kulle wadannan ‘yan jaridar kuma tana bin lamarin sau da kafa.

Mai Magana da yawun maaikatar ta kasashen ketare na Amurka Heather Nauert ta fada a cikin wata sanarwa cewa suna ALLAH waddarai da wannan tsare ‘yan yan jaridan.

Tare da harin da aka kai musu babu gaira babu dalili, domin kawai suna gudanar da ayyukan su kuma suna bayyana ‘yancin su na ikon fadin albarkacin baki.

Dama dai Amurka tasha matsawa kasar ta Sudan data inganta tabioin ta dake da nasaba da fadin albarkacin bakin jamaa,harma da duk wani abu da ya shafi ‘yancin dan adam.

Har ila yau Amurkan bukaci kasar ta Sudan ta tabbatar mutanen nan da take tsare dasu tayi musu adalci.

Kana a rike su dai-dai da abinda dokar kasar ta sudan dama dokar kasa da kasa akan ‘yancin dana dam, suka tanada

Tare da basu damar daukar lauya dama ganawa da iyalansu.

Zanga-zanga da fadace-fadace dai sun barke ne a babban birnin kasar ta Sudan wato Khartoun bayan da kasar ta shinfida wasu matakan tattalin arziki masu zafin gaske, sakamakon umurnin da hukumar bada lamuni ta duniya baiwa kasar kasar.

Abdelmoneim Abu Idris Ali dan shekaru 51 na kanfanin AFP shi da wasu ‘yan jarida biyu ne sai kuma wani wakilin kanfanin dillacin labarai na Reuters, hukumomin kasar suka dauke su ranar laraba lokacinda suka bada rahoton tashin farashin kayayyakin abinci.

Yanzu haka dai ana tsare dasu a sasansani da ake tsare mutane domin binciken su dahukumar bincike da tattara bayanan siri na kasar keyi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG