Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Turkiya Na Kara Karfafa da Fadada Kawance a Nahiyar Afirka


Shugaban Turkiya Recep Tayyip Erdogan da matarsa, Emine Erdogan, a wani biki a Maputo, babban birnin kasar Mozambique,

Sannu a hankali, kasar Turkiya na kara samun tushen zama a nahiyar Afirka, inda take da dumbin ofisoshin jakadanci, sannan take kashe biliyoyin daloli a harkokin kasuwanci a nahiyar cikin shekaru goma da suka shude.

A watan Satumba, kasar ta bude wani sansani soji a Somalia.

Sannan wani sabon matsayi da ta taka shi ne, yadda kasar ta Turkiya ta yi nasarar fadada harkokinta a kasashen da ke yankin kudu da Sahara.

A yanzu haka kamfanin jirgin saman kasar na Turkish Airline, yana zirga-zirga a tsakanin birane sama da 50 da ke nahiyar, baya ga wani katafaren aiki na gina hanyar dogo da kamfanin Yap Merkezi ke yi da za a kashe biliyoyin daloli a tsakanin Ethiopia da Tanzania.

Koda yake kasar ta Turkiya ta fi maida hankali ne kan harkokin tattalin arziki a nahiyar ta Afirka a cewar, David Shin, Malami a jami’ar George Washington da ke sashen nazarin harkokin huldar kasa da kasa a nan Amurka.

A wani rubutun fadin ra’ayi da gidan talbijin na Al Jazeera ya wallafa a bara, shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, ya ce “mutane da dama, suna alakanta tsananin talauci da nahiyar Afirka da tashe-tashen nankula,” amma a cewar Erdogan, su suna kallon nahiyar da idon basira domin Afirka ta wuce yadda ake tsammaninta.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG