Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Turkiya Na Neman Sasantawa da Amurka


Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan
Shugaban kasar Turkiya Racep Tayyip Erdogan

A 'yan kwanakin nan kasashen Turkiya da Amurka sun shiga wani takunsaka da ya kaisu ga zaman dar dar saboda sun dakatar da bayar da takardun shiga kasashensu lamarin da ya soma shafar harkokin arzikin Turkiya

Kasar Turkiyya na neman a dawo da dangantakar dake tsakaninta da Amurka kamar yadda take a can da, biyo bayan zaman ‘dar-‘dar din dake tskanin kasashen biyu kawaye a kungiyar tsaro ta NATO.

Da yake jawabi ga gwamnonin lardunan kasar a Ankara, Faray Ministan Turkiyar,Binali Yildirim, ya ce “fatanmu shine dangantakar dake tsakaninmu ta dawo yadda take cikin gaggawa. Turkiyya ba zata ki amfani da tunani ba alokacin da ake samun sabani ba.”

Dangantakar kasashen biyu dai ta yi rauni biyo bayan kama wani ma’aikacin ofishin jakadancin Amurka, Metin Topuz, wanda ake tuhumarsa da laifin ta’addanci, dake alaka da yunkurin juyin mulkin da bai samu nasara ba a shekarar da ta gabata ga shugaban Turkiya,Recep Tayyip Erdogan.

Zaman tankiyar dai yayi sanadiyar kasashen biyu sun dakatar da bayar da visa tsakaninsu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG