Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Turkiya Tana Taimakawa Kurdawa dake Yaki da ISIS


Ministan Harkokin Wajen Turkiya Mevlut Cavusoglu

A kokarin hana yakin da kurdawa suke yi da ISIS ketare iyaka shiga kasar Turkiya mahukuntan kasar yanzu suna taimakawa kurdawan.

Kasar Turkiyya ta bada sanarwar cewa tana taimakawa kurdawa daga Iraqi su tsallaka cikin Syria, domin su kai ‘dauki’ ga mayakan sakan kurdawa da suke fafatawa da mayakan sakan kungiyar ISIS, wadanda suke dannowa kan garin Kobani.

Sanarwar da ministan harkokin wajen Turkiyya Mevlut Cavusoglu ya bayar, ta zo ne a dai dai lokacinda Amurka take cewa ta samar da makamai da albarusai da kuma kayan jinya ko kiwon lafiya, da hukumomin kurdawa a Iraqi suka samar, ta wajen wurga musu kayan daga jiragen sama a kudancin yankin dake kan iyakar Syria da Turkiyya.

Minista Cavusoglu`bai yi wani karin bayani kan Karin tallafi da Turkiyya take baiwa kungiyar mayakan sakan kurdawan da ake kira Peshmerga ba. Sai dai yace hukumomin kasar da suke Ankara, suna son kawarda duk wata barazana akan yankin kan iyakarta, saboda haka tana hada kai da rundunar taron dangin da Amurka take yiwa jagoranci a yaki da kungiyar ISIS.

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG