Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Venezuela Ta Bayyana Takaicin Ta Na Sata Jerin Kasashe Takwas Da Amurka Tayi.


Mideast Iran Venezuela Russia GECF Summit

Ministan harkokin kasar waje na kasatr Venezuela yayi ALLAH waddarai da saka kasar cikin jerin wadanda ba zasu sha da dadi ba muddin suka yi yunkurin shigowa Amurka

Ministan harkokin wajen kasar Venezuela yasa kafa yayi fatali da saka kasar daga cikin kasashen da zasu dandana kudarsu idan suna son shigowa nan Amurka.

Yace Shugaba Trump yayi kamar wani mai mulkin duniya ne a wajen taron MDD wanda aka kammalaa cikin satin data shige.

Yace, wannan zauren MDD da aka samar da shi domin inganta zaman lafiya amma shi yayi anfani dashi a matsayin wurin ruruta wutar yaki.

Jorge Arreaza Monstserrant yayi wannan kalamin ne sailin da yake jawabi ga mahalarta taron na MDD wanda aka kamala jiya littini.

A cikin satin data gabata ne dai shugaba Trump ya gargadi Korea ta Arewa cewa irin tabi’oin ta zai iya kaita ga halaka.

Arreza dai yana Magana ne akan kalaman da shugaban Trump yayi a ranar 11 ga wata Agusta da yake cewa bai debe tsammani anfani da karfin soja ba, akan gwamnatin Nicholas Muduro wadda take kara jaddada ikon ta ga kasa.

Amurka dai dai ta kakabawa shugaban kasar ta Venezuela takunkunmi dama sauran wasu da yawa daga cikin tsoffi dama shugabannin dake kan karagar mulki yanzu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG