Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashe Da Dama Zasu Sami Cigaba


OECD

Kungiyar Hadin Kan Bunkasa Tattalin Arziki da Kawo Cigaba (OECD) za ta rage kiyasin cigaba da a baya ta ce za a samu a duniya a wannan shekarar, to amma ta na kyautata zaton za a sami cigaba a kasashe da dama a badi.

Kwararru a kungiyar ta OECD sun ce tattalin arzikin duniya zai karu da kashi 3.4% a wannan shekarar, wanda ya dan gaza kiyasin da aka yi a baya.

Kungiyar ta OECD ta kusnhi kasashe 34 da akasarinsu masu karfin tattalin arziki ne.

Kwararru a kungiyar sun ce tattalin arzikin China zai dan lafa, amma zai kai 7.4%. Bincikin ya nuna cewa kasashe 18 daga cikin masu amfani da takardar kudi ta Euro za su dan cigaba fiya da yadda aka zata a baya, ta yadda zai kai 1.2%. Cigaban Amurka zai lafa da .3% zuwa 2.6 a shekarar.
XS
SM
MD
LG