Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Afirka Na Mayar Da Martani Akan Kalamun Shugaban Amurka


Shugaban Amurka Donald Trump

Makon jiya ne shugaban Amurka Dolad Trump ya kira kasashen Afirka da na Haiti wulakantattu yayinda yake ganawa da wasu 'yan Majalisar Dokokin kasar a fadarsa ta White House akan sasanta dokokin shiga kasar

Afrika ta Kudu itace kasa ta baya-bayan nan da ta kira jakadan Amurka a kasarta da yazo yayi bayani akan munanan kalaman da shugaban Amurka yayi amfani dasu akan baki 'yan kasashen Afrika da Haiti a Amurka.

Trump ya bawa ‘yan majalisa mamaki a wani zaman tattaunawa da akayi akan baki ‘yan kasashen waje dake shigowa Amurka, inda rahotanni da yawa suka bayyana cewa ya tambaya “mai yasa muke barin mutane daga wadannan wulakantattun kasashe suke zuwa kasarmu?”

Shugaban ya ce ya kamata Amurka ta fi barin mutane daga kasashe kamar Norway su shigo. Akasarin mutanen kasar Norway turawa ne inda kuma akasarin mutanen Afrika da Haiti bakake ne.

Bayanai daga kungiyoyin kasa da kasa da na cikin gida na nuna damuwa akan yadda Amurka da shugabanta ke komawa hanyar wariyar launin fata. Amma shugaban ya musanta zargin da ake yi masa na cewa yana kin jinin bakake da kuma kalaman da aka ce ya fada.

Hukumar harkokin kasashen duniya ta Afrika ta kudu (DIRCO) za ta yi wani zama a yau Litinin tare da wani na biyu mafi girma a ofishin jakadancin Amurka dake Pretoria akan abinda shugaba Trump ya fadi.

Hukumar DIRCO, a wani bayani da ta bayar, ta ce dangantaka tsakanin Afrika ta Kudu da Amurka da kuma Afrika da Amurka dole sai ta zama bisa mutuntawa da fahimtar juna.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta ce an kira jakadun Amurka a kasashen Haiti da Bostwana da su je su yi bayani akan abinda shugabansu ya ce.

Jakadun Afrika a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, sun bayya mamaki kuma sun yi Allah wadai da wadannan maganganun kin jinin wani jinsi da wariya da shugaban Amurka ya yi, tare da kiransa da ya janye kalaman, ya nemi gafara.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG