Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Da Suka Yi Fice a Fagen Kwallon Kafa A Duniya


Tutocin kasashen da za su je gasar cin kofin duniya ta FIFA a Qatar a watan Nuwambar 2022
Tutocin kasashen da za su je gasar cin kofin duniya ta FIFA a Qatar a watan Nuwambar 2022

Shirin ya duba jerin sunayen kasashen da suka yi fice a fagen taka leda da kuma sunayen kasashen Afrika da matsayinsu a fagen buga kwallo a duniya. Bayan haka, shirin ya duba batun ce-ce-ku-cen da ke faruwa a fagen siyasar neman shugabancin hukumar kwallon kafa ta Najeriya

BAUCHI, NIGERIA - A jerin kasashen da suka yi fice a fagen wasan kwallon kafa, kasar Brazil ce a sahun gaba, Belgium ta biyu, Argentina ta uku, Faransa ta hudu, Ingila ta biyar, Sifaniya ta shida, Italiya ta bakwai, Netherland ta takwas, Portugal ta tara, a yayin da kasar Denmark ta zo matsayi na goma, a cewar hukumar FIFA.

Hukumar ta kuma ce a kasashen Afrika, kasar Senegal ita ce ta shatakwas a fagen tamaula a duniya, sai Morocco ta ashirin da biyu, Tunisia ta talatin, Najeriya ta talatin da daya, Kamaru ta talatin da takwas, Masar ta arba'in, sai kuma Algeria ta arba'in da daya.

A gefe guda kuma, yayin da Amaju Pinnick ke shirin sauka daga mukamin shugabancin hukumar kwallon kafa ta Najeriya da ake kira NFF a takaice, bayan shekara 8, hukumar na ci gaba da shirye shiryen zaben wanda zai maye gurbinsa da za a yi ranar 30 ga watan Satumba.

Ahmed Sani Toro, tsohon babban sakataren hukumar kwallon kafa a Najeriya, yace kwamitin zaben da hukumar ta kafa ya fidda sunayen masu neman takarar kujerar su daya, ciki har da ‘yan arewacin Najeriya shida. Ya kara da cewa ya zuwa yanzu zai yi wuya a yi hasashen wanda ake gani zai lashe zaben.

Saurari rahoton takaitattun labaran wasanni daga Abdulwahab Muhammad:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:07 0:00

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG