Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen dake yankin Tekun Guinea sun yi taro akan tsaro da hadin kai.


Shugabannin kasashen gabar Tekun Guinea sun yi taron tsaro da hadin kai a Abuja
Shugabannin kasashen gabar Tekun Guinea sun yi taron tsaro da hadin kai a Abuja

Kasashe takwas dake gabar Tekun Guinea sun yi taronsu a Abujan Najeriya inda kasar ta karbi shugabancin kungiyar daga kasar jamhuriyar Guinea

Yayinda yake gabatar da jawabi a wajen taron shugabannin kasashen yankin gabar Tekun Guinea, mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ya maida hankali akan batutuwan da suka shafi tsaro da hadin kai.

Farfesa Osinbajo yayi ga kira shugabannin kasashen da su sabunta kokarinsu wajen sake sabunta kuzarin hukumar gabar tekun Guinea domin ta zama abokiyar tafiya a duka kokarinsu a matakin kasa, shiya ko kasa da kasa. Hakan zai sa a tabbatar da tsaro, da samun zaman lafiya da kuma ci gaba mai dorewa ga kasashensu da jama’arsu da sauran masu ruwa da tsaki a shiyar, inji Farfesa Osinbajo.

Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya jagoranci tawagar kasar zuwa taron kasashen gabar Tekun Guinea
Mataimakin shugaban Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo wanda ya jagoranci tawagar kasar zuwa taron kasashen gabar Tekun Guinea

Yanzu Najeriya ta karbi jagorancin kungiyar mai kasashe takwas daga Jamhuriyar Guinea.

A wajen taron, harkar tsaro ce take bakin duk wadanda suka yi jawabi

Manjo Janar Babagana Monguno mai ba shugaban Najeriyashawara akan harkokin tsaro yace Najeriya ta ci gaba da karfafa sojojinta musamman mayakan ruwa domin tunkarar duk wani kalubalen tsaro.

Babbar sakatariyar hukumar Tekun Guinea Uwargida Adenike Ogunko ta nemi hadin kan kasashen dake cikin kungiyar, da su cika alkawuransu na bada kudaden karo karo domin samun gudanar da ayyukan sakatariyar kungiyar

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:14 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG