Amurka da Japan da sauran kasashen duniya na ta tura jiragen sama don kwasar mutanensu daga garin Wuhan da ke yankin tsakiyar China.
A yankin na Wuhan aka fara samun barkewar cutar murar nan da ta zama annoba a duniya baki daya, wadda ta kashe mutane 106 zuwa yanzu.
Japan ta tura wani jirgin sama samfurin jet zuwa Wuhan a yau dinnan Talata don kwasar wajen mutum 200 daga cikin Japanawa 650 da ke birnin.
Amurka kuma na shirin gudu da ma’aikatanta da ke karamin ofishin jakadancinta a Wuhan, tare da sauran Amurkawa, wani lokaci a wannan satin.
Faransa da sauran kasashe ma sun bayyana shirinsu na kwasar ‘yan kasashensu daga yankin.
Hukumomin lafiyar China sun bayyana cewa an samu karuwar wadanda suka mutu wajen 25 a yau dinnan Talata, ciki har da mutum na farko da ya mutu a Beijing babban birnin kasar.
Facebook Forum