Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Duniya Su Guji Ruruta Wutar Rikicin Isra’ila Da Falasdinawa - Jonathan


Tsohon Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, a lokacin da ya kai ziyara Gambia (Twitter/ State of Gambia)

“Abin da ake bukata cikin gaggawa shi ne tsagaita wuta, sai kuma samar da daidaito da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu.”

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan ya yi kira ga Isra’ila da Falasdinawa, da su kai zuciya nesa su rungumi shirin tsagaita wuta.

A wani sakon Twitter da ya wallafa a ranar Litinin, Jonathan ya ce kamata ya yi kasashen duniya sun mayar da hankali wajen sasanta tsakanin bangarorin biyu ba a rika ruruta rikicin ba.

“Ina kira ga kasashen duniya, da su mayar da hankalinsu wajen kashe wutar rikicin, ba ruruta ta ba.” Jonathan ya ce.

Ya kara da cewa, “abin da ake bukata cikin gaggawa shi ne tsagaita wuta, sai kuma samar da daidaito da fahimtar juna a tsakanin bangarorin biyu.”

A cewar tsohon shugaban Najeriya, “abin da ya kamata kasashen duniya su mayar da hankali akai kenan – zaman lafiya, abu ne da zai yiwu.”

Karin bayani akan: Gaza, Isra’ila​, Goodluck Jonathan, Nigeria, da Najeriya.

Goodluck Jonathan ya kara da cewa, “na taba zuwa duka yankunan Isra’ila da Falasdinu, hakan ya ba ni damar fahimtar abubuwan da kowane bangare ke fuskanta.”

Tun da aka fara tarzomar a ranar 10 ga watan Mayu, akalla Falasdinawa 197 aka kashe ciki har da yara kanana 58 da mata 34 a cewar ma’aikatar kiwon lafiya a yankin Gaza.

Akalla Yahudawa 10 aka kashe a hare-haren roka da aka harba a yankin, ciki har da yaro dan shekara shida.

Dubi ra’ayoyi

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG