Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen ECOWAS Sun Tura Dakarunsu Senegal Domin Tilastawa Jammeh Ya Bar Mulkin Gambia


Shugaban Gambia Yahya Jammeh wanda wa'adin mulkinsa ya kare yau Alhamis

Tunda shugaba Yahya Jammeh ya ki sauka cikin ruwan sanyi kasashen Yammacin Afirka na kungiyar ECWAS sun tura wasu dakarunsu kasar Senegal, kasar da ta kewaye Gambia kuma tana yiwuwa su tsunduma cikin Gambian yau

Tuni Najeriya ta aika da jiragen yaki kasar Senegal domin zaman shirin ko ta kwana.

Babban hafsan hafsoshin sojojin saman Najeriya Air Marshall Baba Abubakar yace wannan yakin kawar da Yahya Jammeh yaki ne a karkashin ECOWAS saboda haka hafsan hafsoshin Najeriya ne ya kamata yayi cikakken bayani.

Amma daraktan labarai na hedkwatar tsaron Najeriya Birgediya Janar Rabe Abubakar yace su kam sun shirya tsaf umarni kawai suke jira.

Farfasa Al-Mustapha Osigi na fargaban yin anfani da karfin soji saboda 'yan tawayen Senegal dake makwaftaka da Gambian ka iya marawa Jammeh baya su dagula alamura. Yace idan ma an fitar da Jammeh da karfin soji kotun kolin kasar tace ta rushe zaben yaya ke nan za'a yi.

Farfasa Osigi ya kwatanta abun da ya faru a Gambia da kasar Ivory Coast inda shugaban kasar ya ki sauka sai da aka fitar dashi da karfin soji amma yace a cigaba da lallashinsa ya sauka.

Sai dai Dr. Huseni Abdullahi ya gargadi yin anfani da karfin soji da fatan tsakanin yau zuwa gobe Yahya Jammeh ya canza ra'ayi ya sauka.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:35 0:00

Arewa A Yau

Arewa A Yau
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:00:47 0:00
XS
SM
MD
LG