Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasashen Renon Ingila Suna Taro A London


Queen Elizabeth II shugabar Commonwealth, kungiyar kasashen da Ingila ta yiwa mulkin mallaka
Queen Elizabeth II shugabar Commonwealth, kungiyar kasashen da Ingila ta yiwa mulkin mallaka

A taron kasashe renon Ingila da ake yi a London wakilai daga nahiyar Afirka suna halartar taron

Wakilai daga kasashen nahiyar Afrika suna halartar taron kungiyar Commonwealth a birnin London da taken “abinda ya shafi kowa”.

Batutuwan da za a tattauna a kai sun hada da, sauyin yanayi da inganta damawa da kowanne jinsi.

Maria Fernandez De la Vega, shugabar cibiyar matan Afrika ce ta gabatar da jawabin bude taron.

Tace a wannan lokaci da ake fuskantar rashin ba kowa dama ta bai daya, tilas ne mu ci gaba da tada muryarmu a kan wannan batun. Tace hada hannun matasa da kuma mata zai bamu damar maida hankali kan Afrika.

Cibiyoyi kamar MDD da kuma KTA suna Magana a kan batun bada dama ta bai daya ga kowanne jinsi.

Kasashen kungiyar commonwealth, kasashe renon ingila ne, Birtaniya kuma tana kokarin sake kulla dangantaka da kasashen musamman a wannan lokacin da ta fice daga KTT.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG