Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashi 13% Na Kananan Yara Dake Mutuwa Na Faruwa a Kasar Nigeriya


Wadansu 'yan yara
Wadansu 'yan yara

Kashi 13% na kananan yaran da suke mutuwa kafin su cika shekaru biyar suna faruwa ne a Nigeriya domin rashin tsabta.

Kashi 13% na kananan yaran da suke mutuwa kafin su cika shekaru biyar suna faruwa ne a Nigeriya domin rashin tsabta.

Michael Ojo, wakilin wata kungiyar kasa da kasa mai zaman kanta a Najeriya Wateraid ne ya bayyana haka. Mr. Ojo ya bayyana haka ne a wajen bukin ranar Wanke Hannu ta duniya, wanda ake kiyayewa a dukan duniya a ranar15 ga Oktoba, kowacce shekara.

Mr. Ojo ya kara fadi cewa, kusan yara 100,000 da ke shekara biyar da kasa ke mutuwa a Nigeriya kowacce shekara, kuma kimanin 75,000 na wannan mutuwa za’a danganta shi da batun rashin tsabta na kasar musamman wajen ruwan sha.

Ya ce, za’a iya kauda wanan matsalar da kuma rage yawan mutuwar, idan mutane suka sami ilimi ta wajen tsabta da lura da wurin zaman su. Wanke hannu da sabulu ko kuma toka a lokuta bayan amfani da dakin bayan gida, kamin cin abinci, musamman bayan tsabtace gidan kaji da kuma wankin bayan gidan yaro. Ya bayanna cewa wanke hannu na duniya ba anyi shi domin rage mutuwa kawai ba, amma da yanayin shaka da cututtukan idanu.

Mr. Ojo yace bincike ya nuna cewa a kasashe dake tashi, ba rashin sabulu bane damuwar, amma domin ba’a amfani da sabulu wajen wankin hannu. Domin tabbatar da ci gaban wannan hali na wanke hannu da sabulu ya tabbata, dole ya zama manyan halayen tsabta cikin shirye shiryen Nigeriya.

Ya kara bayanna cewa wannan damuwan ba a kauyuka bane kawai, inda aka dauki mutane marasa ilimi ba. Don ko cikin masu ‘ilimin’ da manyan masu ilimi, yawancinsu basu dauki wannan hali ba na wankin hannuwansu bayan sunyi amfani da bayan gida. A wurare kamar makarantu da asibitoci, ofisoshi da wurin masauki, wurin yin shawara da wuraren sujada inda ake shan hannu, musayar kudi da sauransu.

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG