Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kashim Shattima Ya Roki Mutane da Karsu Yiwa Jonathan Ihu.


Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.
Gwamnan jihar Borno Kashim Shettima.

A ziyarar kanfe da shugaba Jonathan yakai a jihar Borno gwamnan jihar Kashim Shattima ya gargadin jama’ar jihar Borno dama magoya bayan jamiyyar APC, da guji nuna rashin da’a ga shugaba Goodluck Ebele Jonathan na Najeriya dama mukarabban sa wadanda zasu ziyarci jihar, domin kadda mar da yakin neman zaben sa.

Wannan gargadin ya biyo bayan shirin da Shugaba Jonathan din yayi domin ziyarar jihar Borno domin kaddamar da yakin neman zaben sa, kwanaki 10 kenan da shugaba Jonathan din ya ziyarci jihar Borno, inda ya gana da jamiaan soja da sansanin yan gudun hijira dake cikin garin Maiduguri, inda ya jajantawa jamaar jihar.

Wannan gargadin ba zai rasa nasaba da abubuwan da suka faru a jihar Katsina da Bauci ba, inda wasu matasa suka dinga ature ga shugaban kasar, sai wannan sanarwan da gwamnan ya rattabawa hannu da mai bashi shawara a harkokin yada labarai Umar isah Gusau ya aikewa manema labarai ta yanar gizo yana cewa ga dukkan bayanan da ya samu wannan ya faru ne a jihohin daba jamiyyar APC ke mulki ba, kuma bai son hakan ya faru, duk ko da suna da nasu bambamce bambance siyasa amma fa duk shugaba shugaba ne a cewar gwamna.

Ko a wancan ziyarar da shugaba Jonathan ya kawo garin Maiduguri sai da wasu matasa suka nuna goyon baya ga wani dan takara na daban, wanda wancan likacoin ma sai da gwamnan jihar Kashin Shattima yaja hankulan matasar, yana mai cewa a al’adar mu na mutanen arewa muna girmama shugabanni, ina rokon ku duk wanda ke kaunar Borno duk wanda ke kaunar zaman lafiya mu bashi goyon baya da darajjar da ALLAH ya bashi, don mulki daga wajen ALLAH ne.

Gwamnan yace dan ALLAH kar a sawo maganar da bata dace ba , sai dai gwamnan yace ba wata sanarwan takaita zirga-zirgan da akayi , sai dai Al’ummar jihar na cike da fargaba domin ganin a waccan ziyarar an takaita zirga-zirga.A inda yan makaranta da yan kasuwa suka wahala sosai.Da kuma rufe hanyoyi da akayi ba tare da wata sanarwa ba. Wannan yasa wasu yan jihar jan hankulan jamiaan tsaron jihar da babbar muryar cewa suwa ALLAH su taimaka musu suci gaba da gudanar da harkokin sun a neman cin abincin su, a cewar wasun su saui sun fita ne zasu samu abinda zasu sa a baka.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG