Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwanni Saka Jari Sun Fi Son Hillary Clinton Ta Ci Zaben Amurka


Kasuwar hada-hadar hannun jarin kamfanoni ta New York
Kasuwar hada-hadar hannun jarin kamfanoni ta New York

Makon jiya da hukumar FBI tace zata cigaba da binciken Hillary Clinton hannun jarin kasuwanni duniya sai suka fadi amma da hukumar kuma tace babu wani laifi da ta gano ta kuma wanke Hillary Clinton sai kasuwaanni suka yi sama

Hannayen Jari a Amurka da Turai da kuma Asia sun tashi biyo bayan hurucin hukumar binciken manyan laifuka ta FBI cewar bata samu wani abin da zai sa ta gabatar da yar takarar Democrat Hillary Clinton gaban shara’a ba, dangane da sabbin sakwanninta na email.

Masu zuba jari sun bayyana fargabansu a kan kila Donald Trump na Republican zai yi nasarar lashe zabe wanda kuma hakan ya sa hannun jari ya yi kasa saboda hurucin darektan hukumar FBI a waccan mako cewar zasu kaddamarda wani sabon bincikin sakwannin Hillary Clinton na email.

A jiya Litinin da rana darajar hannayen jari ta yi sama da kashi 1.5 cikin dari da ma sama da hakan. Wasu ýan kasuwa na ganin alkawarin da Trump ya yi na canja tsarin Amurka a kan cinikayya da haraji zai sa darajar dala Amrka ta fadi.

XS
SM
MD
LG