Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Fara Ganin Koma-baya A Kasuwar Hada-hadar Kudaden Duniya


Wurin da ake musayar kudi a Istanbul babban birnin Turkiya
Wurin da ake musayar kudi a Istanbul babban birnin Turkiya

Matsalar da tattalin arzikin kasar Turkiya ke fuskanta ta fara shafar kasuwar hada hadar kudaden duniya makon jiya inda darajar kudaden China, Brazil da Mexico ta raunana yayinda kasashen Turai dake taimakawa Turkiya su ma darajar kudadensu ta fadi warwas

Kasuwar hadahadar kudade ta duniya ta fara fuskantar koma-baya a makon da ya gabata, yayin da matsalar da tattalin arzikin Turkiyya ke fuskanta, ta haifar da sabuwar fargabar cewa akwai yiwuwar tasirin komadar tattalin arzikin kasar, ya fadada har ya kai ga karayar tattalin arzikin duniya, kamar yadda aka gani a shekarar 2008.

Farashin hannayen jarin bankunan nahiyar turai da manyan masu bai wa Turkiyya bashi, sun fadi warwas, sannan kudaden China, Brazil da Mexico duk sun raunana.

Masu fashin baki da dama na fadin cewa, babban tasirin komadar tattalin arzikin na Turkiyya kan basussukan da ake bin kasar da faduwar darajar kudin kasar, zai zamanto takaitacce, inda mai yiwuwa Burtaniya ta fi kowacce kasa makuwa daga wannan matsala, saboda bankunan kasar da dama, su suka fi ba kasar ta Turkiyya basussuka, kamar yadda masanin tattalin arziki a bankin Deutsche, Oliver Harvey ya fada.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG