Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasuwar Hannayen Jari Ta Fadi a Yankin Asiya


Kasuwar hannayen jari a yankin Asiya ta fadi a ranar Alhamis, sanadiyyar shiga yanayi na damuwa da babban bankin Amurka ya yi, kwana guda yayin da yake kokarin farfadowa daga tasirin annobar coronavirus. 

A Japan, kasuwar hannaye jari ta Nikkei ta fadi da kashi daya cif.

S&P/ASX ta yi kasa da maki 0.7. A Korea ta Kudu, kasuwar KOSPIA ta fadi da kashi 3.6 kana TSEC ta Taiwan ta yi kasa da kashi 3.2.

A can Hong Kong kuwa, kasuwar hannayen jari ta Hang Seng ta ci kasuwarta ne da faduwar kashi 1.8, yayin da Composite ta Shanghai ta yi kasa da kashi 1.3 ita kuma Sensex ta Mumbai ta fadi da kashi daya.

Wata takardar da ta nuna abubuwan da aka tattanauna a taron da babban bankin na Amurkan ya yi a watan da ya gabata, wacce aka fitar a jiya Laraba, ta nuna mambobin bankin da dama sun nuna damuwa kan tasirin annobar.

“Za ta ci gaba da yin tasiri akan harkokin tattalin arziki, ayyukan yi, da hauhawan farashin kayayyaki, har nan da zuwa wani lokaci, hakan kuma na iya zama barazana ga daukacin tattalin arzikin har nan da zuwa wani matsakaicin lokaci.” mambobin suka ce.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG