Accessibility links

Kungiyar Alkalan shari'ar sun bayyana cewa ana musu shiga sharo ba shanu a al'amuran shari'ar kasar da sunan siyasa.

Kungiyar Alkalan shari’a a Nijar suna kokawa game da yadda wasu jami’an gwamnati ko ‘yan siyasa ke katsalandan a harkokin shari’a.

Kungiyar ta alkalan shari’a ta nuna bukatar ya kamata a kakkama wadanda aka san suna katsalandan din ga huklumar shari’a don a hyukunta su.

Har ma suka nuna rashin jin dadinsu ga yadda Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou ya zura ido yana kallo wasu ciki har da mukarrabansa na tsomawa sharia baki a al’amuranta.

XS
SM
MD
LG