Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Katsewar Intanet: Kamfanonin Sadarwar Na Kokarin Dawo Da Ayyukan Intanet A Cewar Hukumar NCC


Subsea Cable
Subsea Cable

Hukumar NCC mai kula da harkokin sadarwa a Najeriya tace kamfanonin sadarwa na kokarin dawo da sadarwar intanet bayan data katse a jiya Alhamis.

Katsewar wayoyin sadarwa a karkashin teku ya jefa kamfanonin sadarwar nahiyar Afrika cikin gararin katsewar ayyukansu

Masu amfani da na'urorin sadarwa da bankuna sun tsinci kansu cikin garari tsawon sa'o'i sakamakon katsewar intanet wacce ta kassara harkokin sadarwa da hada-hadar kudi.

Saidai da sanyin safiyar Juma'ar nan, Hukumar NCC tace ana kokarin magance matsalar.

Sanarwar da Daraktan yada Labaran Hukumar NCC, Reuben Muoka ya fitar ta bayyana cewar "tuni hukumomin dake kula da wayoyin sadarwar karkashin teku sun fara aikin gyaransu, kuma a hankali ayyukansu na dawowa".

“Hukumomin sun sha alwashin yin aiki ba dare ba rana domin dawo da sadarwar intanet a kasashen da al'amarin ya shafa nan da dan kuma cikin kankanin lokaci. Abu ne mai mahimmanci mu sanarda kamfanoni da daddaikun mutanen dake hulda damu game da halin da ake ciki".

HAkazalika, Hukumar NCC ta bayyana cewar katsewar wayoyin da suka yi sanadiyar lalacewar na'urorin dake karkashin teku, sun yi mummunan tasiri akan ayyukan sadarwar intanet dana wayar tarho a kasashen yammacin nahiyar Afirka ciki harda Najeriya da Ghana da Senegal da Cote'd Ivore.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG