Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kayan Sa Maye Na Matukar Barna Ga Jama'a


Wasu kayan sa maye da aka kama
Wasu kayan sa maye da aka kama

Yayin da matasa ke kafa hujja da dalilai dabandaban na shan kayan maye da su ke yi, kwararru sun bayyana illoli masu muni da kayan mayen ke haddasawa

Wasu matasa sun ce sun shiga shayeshaye ne saboda dauke kewa da bacin rai kan irin rashin da su ke fama da shi. Su ka ce sam ba su jin dadin garin, saboda hatta iyayensu a wahale su ka taso. Don haka su ka ce kwayar ce kawai ke kwantar masu da hankali. Don haka muddun babu ita to babu zaman lafiya.

Wakilinmu na Kano da ya yi hira da matasan Mahmud Ibrahim Kwari ya ce baya ga matasan da ke kafa hujja da rashin ayyukan yi, hatta wasu manyan mutane ciki har da ‘yankasuwa da ma’aikatan gwamnati da matan aure na ta’ammali da kwayoyi bisa dalilai dabandaban.

To saidai Dakta Musa Gambo Takai na Sashin Kula Da Masu Lalurar Kwakwalwa na Asibitin Koyarwa na Aminu Kano ya zayyana illolin amfani da duk wani kayan maye. Illolin sun hada da na kwakwalwa da ciwon hanta da ciwon hanta da ciwon matuwa da shanyewar jiki da kuma nakkasa jariri (ko dan tayi) gabanin haihuwarsa. Wannan kuwa bayan ga yawan haddasa hauka ne da kwayoyin ke yi, in ji shi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:22 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG